An mayar da gwamna Danbaba Suntai gida a Jalingo jahar Taraba daga wani asibitin birnin London. Gwamnan ya koma gida ne a daidai lokacin da Majalisar zartaswar jahar ta bukaci kafa wani kwamitin kwararru na mutum biyar ya binciki lafiyar gwamnan wanda ke jinya tun shekarar dubu biyu da goma sha biyu bayan hatsarin da yayi a jahar Adamawa a cikin karamin jirgin saman shi da yake tukawa da kan shi a lokacin.
Da safiyar nan ta Litinin an sanya garin Jalingo cikin shirin ko ta kwana inda 'yan sanda suka yi ta shawagi cikin motocin su bisa la'akari da alamun da mukarraban gwamna Danbaba suka nuna cewa zai shiga ofis.
A daidai wannan lokaci ne kuma cece kuce da cacar baki dajifan juna da kalamai suka dada kunno kai a jahar tsakanin masu ra'ayin cewa Gwamna Danbaba Suntai ya warke an sallame shi daga asibiti kuma zai koma aiki, da kuma masu ra'ayin cewa ba ki suka yi gwamnan ya koma ofishin shi ba, amma da farko kwararru su yi binciken tabbatar da cewa gwamnan ya na da koshin lafiyar iya ci gaba da mulkin jahar. Kamar dai yadda za ku ji bayani a cikin rahoton da Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga Jalingo, babban birnin jahar taraba.