Shugaban hukumar Kwastam na tashar Tin-Can Alhaji Bashar Muhammad, yace an kama manyan bindigogi biyu da harsasai 7,500 sai kuma sulke da hular kwano da takalma, wanda duk wani ‘dan Najeriya yayi kokarin shigar da kayan.
Yanzu haka dai hukumar Kwastam sun mika mutumin da suka kama ga hukumar tsaro ta DSS domin gunadar da bincike a kansa.
A cewar Alhaji Bashar Muhammad, anyi kokarin shigowa da kayayyakin ne ta hanyar amfani da kwantainar da gwamnati ta baiwa duk wani ‘dan Najeriyar da ya zauna a wata kasa a kalla watanni tara damar shigowa da kayansa ba tare da ya biyawa kayansa haraji ba.
Domin karin bayani saurari tattaunawar da shugaban Kwastam Alhaji Bashar Muhammad.