A halin da ake ciki kuma, 'yansandan Canada sun kama wani dan asalin kasar Somaliya, wanda ya kade wani dan sanda da mota a wajen wani filin wasan kwallon kafa da ke Edmonton, sannan ya yi ta daba ma dansandan wuka kafin ya gudu. Daga bisani, mutumin ya buge wasu matafiya da wata motar daukar kaya yayin da yansanda suka fafaro shi da daren ranar Asabar.
Dukkan mutanen biyar din na asibiti saboda raunukan da ba a bayyana yanayinsu ba. Da maharin da wadanda ya hara babu wanda aka bayyana sunayensu ga jama'a.
To amma Marlin Degrand, mataimakin kwamishinan Rundunar 'yan sandan Canada,ya ce wanda ake zargin wani dan asalin Somaliya ne mai neman mafaka irin ta 'yan gudun hijira a Canada. Wanda ake zargin sananne ne ga hukumomin 'yansandan Edmonton da Canada. Degrand ya ce an taba tsai da mutumin aka masa tambayoyi a 2015 saboda tsauraran akidojinsa, to amma bai cancanci tuhuma ba bayan da aka yi masa cikakken bincike.
Shugaban 'yansandan Edmonton, Rod Knecht ya ce wanda ake zargin na da wata tutar ISIS cikin motar da ta kade dansandan. Amma hukumimi sun ce da alamar shi kadai ya aikata harin.
Facebook Forum