A wannan shirin mun yi hira da mawakiya da aka fi sani da Jamsy wadda ke waka da Hausa da kuma larabci.
Mun kuma bada labarin wani malamin makaranta da ya yi ritaya, ya yi amfani da kudin sallamar shi ya sayi keken NAPEP domin biyan bukatun gida na yau da kullum, sauran kudin kuma ya ba matarshi ta yi jari.
Suna nan suna rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da 'ya'yansu hudu sai matar ta kama rashin lafiya kamar ba za ta kai ba, da aka kai ta asibiti sai Likita ya ce ana bukatar a yi mata aiki cikin gaggawa domin a ceci ranta aka kuma bukaci mai gidan ya biya Naira dubu 300 kafin a yi mata aiki.
Mijin ya koma gida ya tattara duk ajiyar da ya yi daga sana'ar keke NAPEP da sauran kudin fanshonsa duka suka tsaya a Naira dubu 275, ya rasa inda zai sami cikon dubu 25. Hankalinsa ya yi matukar tashi, sai ya koma asibitin ya tambayi matar ko tana da wata ajiya daga sana'rta ta ranta mashi ya cika kudin a yi mata aiki kada su rasa ta, sai ta rantse tace ba ta dashi domin ta sayi kayan shago kwanan nan ta kashe abinda ke hannunta duka.
Mijin ya rasa abinda zai yi sai ya yanke shawara ya sayar da keken NAPEP din ya cika kudin asibitin, ya koma ya dauki mabudin keken ke nan ya bufe kofa cikin sauri mabudin ya fadi karkashin gado, ya yi ta kokarin ya zaro amma ya kasa sai ya daga katifa domin ya iya daukar mabudin sai ya ga katifar a yage a gefe wani rui kuma ya yi tudu, ya zura hannu ya ga abinda yayi tudun sai ya tarar ashe matarshi ce ta tsaga yadin katifar tana boye kudinta a ciki, da ya kirga sai ya tarar da naira dubu 200 matar ta boye.
Saurari shirin domin jin yadda aka karasa: