Washington, dc —
A wannan shirin mun kawo kashi na biyu na hirar da wakilinmu a Maradi, Jamhuriyar Nijar, Mansur Sani ya yi da wani fitaccen dan wasan kwaikwayo Adamou Madougou Andige wanda ya shafe sama da shekaru 23 a sana'ar.
Mun kuma bada labarin wani magidanci da ya saiwa matarshi wayar salula mai tsada ya kunshe a takardar cakuleti da tsabar kudi Naira dubu dari biyar, ta dauka ta kyautar ba ta san abinda ke ciki ba:
Saurari cikakken shirin:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.