An kame mutanen ne sakamakon tuhumarsu da a keyi na tada zaune tsaye a yayin wani taron koli na jam'yyar a karkashin jagorancin Husseini Umaru.
Mintoci kadan kafin su kammala taron jami'an tsaro suka yi diran mikiya a kan gidan da aka kuduri aniyar yin taron. Jami'an tsaro sun shaida masu da su watse domin basu samu izinin yin taron ba a hukumance domin maganar MNSD na gaban shari'a.
Malam Ali Sabi mataimakin shugaban jam'iyyar MNSD yace 'yansanda sun far masu suna dukansu suna son su koresu daga yin taron abun da yace doka ta hana. Yace akwai mutane uku hannun 'yansanda. Su ukun su ne Abdu Adamu daga Damagaran da magatakardan jam'iyyar Umaru Hadari wanda suka kama a Kwanni cikin dare da kuma wani a wata anguwa.
Wasu jigajigai masu fada a ji a jam'iyyar MNSD karkashin jagorancin Albadu Abuba sun kirawo manema labaru domin rashin cancantar kiran taron da uwar jam'iyyar tayi a yankin Zinder. A cewarsa kame-kame ne kawai bangaren Husseini Umaru yayi. Wadanda suka gudanar da taron ba'a zabesu ba a shekarar 2009 inji Albadu. Yace tun shekarar 2005 suka yi zabe kuma har yanzu ba'a yi wani ba.
Ita dai jam'iyyar MNSD tana da matsalar cikin gida inda ta dare gida biyu kuma bangaren Albadu Abuba na marawa gwamnatin Muhammad Yusuf baya. Su kuma bangaren 'yan adawa suna da goyon bayan Husseini Umaru.
Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.