WASHINGTON, DC —
Shirin Kallabi na wannan mako ya haska fitila kan wani yanayin rayuwa da Matasa Mata da dama su ke shiga wanda kuma al’umma ke kyamata.
A kasashe da dama na duniya, mutane musamman Matasa suna zuwa gidan Gala da ake kira Club da turanci, domin shakatawa, da saduwa da abokai ko neman kulla abota da masoya, da dai sauransu.
A kasashen nahiyar Afrika da dama, ana daukar masu zuwa gidan Gala a matsayin mutanen da basu da tarbiya, da sukan zama abin kyama har tsakanin danginsu. Shirin kallabi ya yi hira da wadansu Matasa Mata da suke harka a gidan Gala wadanda suka bayyana abinda ya sa su irin wannan rayuwar.
Saurari cikakken shirin:
Dandalin Mu Tattauna