Arsenal ta wallafa yin asarar fam miliyan 17.7 a kakar 2023/2024 duk da dawowarta gasar zakarun Turai ya taimaka wa kungiyar wallafa samun tarin kudin shigar da ya kai fam mliyan 616.
Dawowar kungiyar gasar manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai ya taimaka wajen karuwar kudin shigarta zuwa fam miliyan 71 a bangaren yada labaru da kuma fam miliyan 29 na kudaden da take samu a ranar da take buga wasa.
Haka shima kudin shigar kungiyar a bangaren tallace-tallace yayi matukar karuwa zuwa fam miliyan 218.3 sakamakon sabunta kwantiragi da kamfanin jiragen saman Emirates mai daukar nauyin talla a filin wasa da jikin rigunan ‘yan wasa da kuma sayar da damar sanya wa filin daukar horon kungiyar suna ga kamfanin Sobha Realty.
Sai dai, albashin da kungiyar ke biya ya yi tashin gwauron zabo daga fam miliyan 234.8 zuwa fam milyan 327.8.
Alkaluman raguwa ce a kan asarar fam miliyan 52.1 da aka samu a watanni 12 da suka gabata.
Dandalin Mu Tattauna