Janar Babangida Wanda ke zantawa da manema labarai albarkacin cikarsa shekaru 81 a duniya ya ce hakuri shine babban abinda ya kamata ‘yan kasar su rike domin cin moriyar juna duk da banbancin yare da addini dake a tsakanin al’ummar Najeriya.
A kan matsalar rashin tsaro da ya addabi sassan Najeriya kuwa, Janar Babangida wanda ke cikin yanayi na yawan shekaru ya ce sun fada a baya cewa a ci gaba da addu’a kuma akwai lokacin da lamarin zai zama tarihi ga kasa.
Toshon shugaban ya ce ya sha fada a duk lokacin da zai hadu da jama’a da a kara hakuri saboda wannan halin rashin tsaro ba abu ne mai dorewa ba kuma kowa ya yi Imani cewa lamarin zai kau nan da dan lokaci. IBB ya kuma gargadi masu yin wannan aika-aikar da su daina, su ajiye makamansu kana su tuba.
Tuni dai ‘yan Najeriya suka fara yin tsokaci akan kalaman tsohon Shugaban Alh.Barde Suleja na daya daga ciniknsu. Galibi sun goyi bayan shugaban a kan kiran da ya yin a jinginar da batun banbance banbance a hada kai domin ci gaban kasar.
Duk da yanayi na yawan shekaru dai janar Babangidan na ci gaba da samun manyan baki a gidansa dake kan tsaunin tsakiyar Birnin Minna.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti: