WASHINGTON DC —
Wannan makon shirin Kallabi zai karkata akalar shi ne akan zaben shugaban kasa a Amurka, zaben da za a gudanar da shi a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024. Amurkawa zasu nufi runfunan zabe domin zaben shugaban kasa karo na 60 a takara tsakanin tsohon shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris.
A wannan karon zaben ya dauki hankalin Mata a duk fadin duniya, kasancewa ‘yar takarar Jam’iyyar Democrat Mace ce, kuma takarar Kamala Harris ta zaburar da mata a nahiyar Afrika wandanda suka dade suna neman a dama da su a harkokin mulki. Shirin kallabi zai tattauna akan tasirin zaben Amurka a fafutukar Mata.
Saurari cikakken shirin cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna