WASHIN GTON, DC. —
A wannan karon mun maida hankali kan dokar hana shiga birnin Yamai da amalanken ciyawar dabobi da itacen girki saboda abinda hukumomi suka kira riga kafin dakilen yunkurin shigar da makamai da myagun kwayoyi ta wannan hanya.
Sannan mun dubi takaddamar da ke shirin kunno kai tsakanin kungiyoyin malaman makaranta da gwamnatin Nijer a wani lokacin da ake shirin komawa makarantu bayan kammala babban hutun shekara.
bakin shirin sun hada da Ibrahim Kantama dan jarida a talbijan TAMBARA da Hamissou Abdoulaye dan jarida a talibijan Bonferey kuma manajan Muryar Nijer Web TV.
A saurari shirin tare da Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna