A shirin Kallabi na wanan makon zai duba yadda rashin ilimi ke tasiri akan matsalar karuwar shan miyagun kwayoyi tsakanin matan aure da zawarawa a arewacin Najeriya, inda a Makon da ya gabata Mata ‘yan fafatuka suka haska fitila kan matsalar a cikin shirin.
Batun shan miyagun gwayoyi da rahotanni ke nuni da cewa, yana kokarin shan kan al’umma a arewacin Najeriya da ya shafi matan aure da ‘yan mata, shirin kallabi ya karbi bakuncin Dr. Zarah Yusuf ‘yar fafatuka a Damaturu jihar Yobe, da kuma Aisha Moh’d Yakasai, shugabar kungiyar dake kula da tarbiyar matasa a jihar Kano, wadanda suka bayyana yadda rashin ilimi ke tasiri a ruruta wannan matsalar.
Sannan shirin zai ci gaba da tattauna da Helen Bako wadda ta shafe sama da shekaru 23 tana aikin daya jibanci kula da jin dadi da walwalar Al’umma musamman ma tsakanin Iyali a Amurka. Kuma shugabar wata kungiyar wanzar da zaman lafiya ta Mata da ake kira (Nigerian Women against Violence) dake aiki a ciki da wajen Najeriya, inda ta bayyana tsarin gudanar da aiki a kasashen Nahiyar Afrika da kuma yadda ya banbanta a Amurka.
Saurari cikakken shirin da Grace Alheri Abdu ta gabatar:
Dandalin Mu Tattauna