A shirin Kallabi na wanan makon zai duba yadda yajin aikin yake shafar Mata a cikin gida a Najeriya. Kungiyoyin kwadago sukan shiga yajin aiki a Najeriya da nufin neman hukumomin su biya musu wadansu bukatu da suka jima suna nema, na baya bayan nan shine yajin aikin da manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya suka kira domin neman karin albashi da kuma rage kudin wuta bisa la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar. Ta yaya irin wannan matakin yake shafar Mata a cikin Gida?
Sannan shirin zai haska fitila akan yadda Mata a Arewacin Najeriya suke shiga shan miyagun kwayoyi.
Sannan shirin ya tattauna da Helen Bako wadda ta shafe sama da shekaru 23 tana aikin daya jibanci kula da jin dadi da walwalar Al’umma musamman ma tsakanin Iyali a Amurka. Kuma shugabar wata kungiyar wanzar da zaman lafiya ta Mata da ake kira (Nigerian Women against Violence) dake aiki a ciki da wajen Najeriya.
Saurari cikakken shirin da Grace Alheri Abdu ta gabatar:
Dandalin Mu Tattauna