Yau muke karkare tattaunawar wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka da shugabanin Kungiyoyin Nakasassu da masana sha’anin doka dangane da hanyoyin shigar da masu bukata ta musamman a sahun ma’aikatan kwadago a hukunce ta yadda za a rage yawan masu dogaro da bara a matsayin sana’a.
Tayar da gwamnatin Ghana daga barci game da nauyin da ya rataya a wuyanta akan maganar inganta rayuwar irin wadanan mutane da gudunmowar da ta wajaba masu zaman kansu su bayar ne ya sa shirin Nakasa ya maida hankali kan kudirin dokar da wani wakilin al’ummar kasar ya shigar a gaban Majalissar Dokoki don ganin an kafa dokar da za ta tilasta kebe kashi 5 cikin 100 na guraben aiyukan yi ga mutanen da ke da tawaya.
Zamu ji shawarwarin da shugaban gidauniyar jin dadin Nakasassu ya bayar a kashi na karshe na wannan tattaunawa da Idriss Abdallah Bako ya shirya a birnin Accra.
A saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya gabatar:
Dandalin Mu Tattauna