Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Ya Bukaci Hadin Kan Kasashe Don Yaki Da Ta'addanci a Afrika


Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu

A ranar Litinin 22 ga watan Afrilu ne aka bude wani taro kan yaki da ta'addanci a Afirka a Najeriya, inda daruruwan wakilai daga sassan duniya suka hallara.

Shugabannin da suka halarci taron na fatan a sami sauyi ta hanyar hadin gwiwa da kawance a yankin.

Najeriya da ofishin yaki da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya (UNOCT) ne suka dauki nauyin taron da nufin karfafa matakan tsaro da hadin gwiwa a yankin wajen yaki da ta'addanci.

A yayin jawabinsa a taron, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce “ta’addanci na kawo cikas a duk wani kokarin ciyar da kasa gaba da muke nema wa kanmu da ‘ya’yanmu. Wannan mummunar barazanar na neman tsorata manomi akan gonakinsa, yara akan makarantunsu, mata akan zuwa kasuwa da kuma iyalai akan gidajensu. Don haka ya zama wajibi mu taru mu yi yaki da wannan barazana, mu himmatu a kokarinmu a matakin kasa da samun hadin gwiwa a yankin da ma kasashen duniya,".

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Taron na neman inganta musayar bayanan sirri tsakanin kasashen Afirka da karfafa dabarun yaki da ta'addanci da Afirka zata jagoranta.

Ta'addanci da mummunan tsattsauran ra'ayi na bazuwa sosai a Afirka.

Wani sabon bincike da cibiyar nazarin dabarun Afirka ta yi, ya nuna cewa ayyukan ta'addanci sun karu da fiye da kashi 100,000 a cikin shekaru 20, duk da matakan ciki da waje da aka dauka.

Rahoton ya ce sama da mutane 23,000 ne aka kashe a Afirka a shekarar da ta gabata, karin kashi 20 cikin 100 kenan idan aka kwatanta da shekarar 2022.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo a nasa jawabin, ya ce yaki da ta'addanci ya wuce batun iyakokin kasa, amma "yadda lamuran ta'addanci ke sauyawa na bukatar a dauki matakai daban-daban masu tsauri na hadin gwiwa da suka wuce batun iyakokin kasa da kokarin daidaikun mutane".

Ya kara da cewa ''wadannan kungiyoyin suna amfani da korafe-korafe da raunin jama’a tare da yada akidunsu don haddasa fargaba, rarrabuwar kawuna da kawo rudani. Mun fahimci akwai bukatar gaggawa ta yakar wannan abu da ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya, tsaro da ci gaban nahiyarmu,".

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Hukumomin kasar sun ce barazanar ta'addanci a nahiyar Afirka na kara ta'azzara ne saboda kwararar makamai ba bisa ka’ida ba, da rashin aikin yi, da talauci, da rashin isassun 'yan sanda, da nuna wariya da kuma rikicin siyasa.

Sama da shekaru goma kenan Najeriya ke fafutukar ganin an kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram da 'yan ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kuma a baya-bayan nan, ‘yan bindiga suna kara tsananta lamarin.

Yan Bindiga
Yan Bindiga

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara a harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ya ce akwai bukatar a magance wadannan abubuwa.

"Dabarun da suka dace a dauka na bukatar ingantattun hanyoyin da za su magance wadannan matsalolin, da karfafa habbakar tattalin arziki, da karfafa hadin gwiwar yanki da ta kasa da kasa," a cewar Ridabu.

Amma samun kudaden yin hakan ya zama babban kalubale a Afirka.

Hukumomi na fatan canza lamarin.

Vladimir Voronkov, U.N.
Vladimir Voronkov, U.N.

"Don magance ta'addanci yadda ya kamata, kungiyoyin yankin Afirka suna da muhimmiyar rawar da zasu taka. Nasarar Majalisar Dinkin Duniya a Afirka ta dogara ne akan kokarinmu na tallafa wa kudurorin Afirka don magance kalubalen Afirka. Mun fahimci cewa babu wani bangare daya da zai iya magance barazanar zaman lafiya da tsaro a yau, a maimakon haka akwai bukatar bangarori da yawa su yi aiki tare don cimma burin,” a cewar Vladimir Voronkov, karamin babban sakataren hukumar UNOCT.

An fi ganin ayyukan ta'addanci a nahiyar a yankunan Sahel, Somaliya, tafkin tafkin Chadi, Arewacin Afirka da Mozambique.

Kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ba su halarci taron ba saboda takunkumin da kungiyar ECOWAS da kungiyar Tarayyar Afirka ta AU su ka kakaba musu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi.

Masu sukar lamiri sun ce idan ana so matakan yaki da ta'addanci su yi nasara sosai, to ya zama dole kowace kasa ta shigo cikin lamarin.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG