A wani rahoton da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Neja ta fitar a karshen shekara ta 2023 ya nuna cewa da ga shekarar 2017 zuwa wannan lokaci, sama da garuruwa 335 ne Mutanensu suka tarwatse a cikin kananan Hukumomi 14 na jihar Neja saboda Matsalar Hare Haren 'yan fashin Dajin