Shekaru 400 kenan da bayin farko suka fara sa kafa a kasar nan da yanzu ake kira Amurka. Isowar wani jirgin ruwa dauke da bayi ‘yan Afirka daga Angola a yankin Virginia da ke karkashin mulkin mallakar Birtaniya a watan Agustan 1619, ya bude kasuwar cinikin bayi a Amurka da aka kwashe shekaru sama da 200 ana yi..
Anyi Taron Bukin Shekaru 400 Da Bayin Farko Suka Fara Sa Kafa A Amurka.
Ma'aikatan Muryar Amurka sun ziyarci jami’ar garin Norfolk wato Norfolk State University inda aka kaddamar da taron shirye shiryen bukin tuna fataucin bayi.
Facebook Forum