Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ayyana Kawo Karshen Tsarin Obamacare


Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana kawo ‘karshen tsarin inshorar lafiya ta da ake kira Obamacare, bayan da ‘yan Majalisar Wakilan Amurka suka kada kuri’ar soke ta da kuma maye gurbinta da wani sabon tsari.

Trump dai yayi murnar wannan nasara ta farko da ya taba samu a fadarsa ta White House, zagaye da yawancin ‘yan Majalisar jam’iyyar Republican ‘din da suka kada kuri’ar soke tsarin Obamacare da kuma maye gurbinta.

“Sun yi haka ne domin ‘kasa, ba wai don jam’iyyarsu ba,” a cewar Trump lokacin da yake magana kan ‘yan jam’iyyarsa.

Shi dai wannan sabon tsarin na inshorar lafiyar ya samu nasara ne a Majalisa da kuri’u 217 na wadanda suka amince sai kuma 213 na wadanda basu amince ba. Baki ‘daya ‘yan jam’iyyar Democrat basu amince da kuri’ar ba, tare da wasu ‘yan jam’iyyar Republican 20.

Babban banbanci dake tsakanin tsarin Obamacare da wannan sabon tsari shine na cazar mutanen da suke da matsalar lafiya ‘karin kudi.
Tsarin Obamacare ya haramtawa kamfanonin inshora cajin mutane kudade masu yawa saboda suna ‘dauke da wata cuta. Karkashin sabon tsarin kuwa, jihohi ne ke da hurumin barin kamfanonin inshore su yiwa marasa lafiya tsada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG