Bayan data shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane domin kudin fansa, Rundunar ‘yan Sandan jihar Ogun, ta ceto tsohuwar Ministan Ilimi Mrs. Iyabode Anisoluwa, wanda ta shafe kwanaki bakwai a hannun masu garkuwa ta ita.
Sai dai kawo yanzu kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Lagos, Sufritanda Dolopo Badmus, shima ya bayyana cewa rundunar ta kama wani mutun da ake zargin shine ya shirya batun sace tsohuwar Ministan a jihar ta Ogun, wanda kuma aka kama shi a babban fillin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos, akan hanyarsa ta zuwa Dubai.
Satar mutane dai ba sabon abu bane a tarayyar Najeriya, Alhaji Abubakat Ibrahim Dande, shugaban kungiyar Fulani na Jamnati Fulbe, rashen jihar Ogun ya baya cewa Fulani ma basu tsira ba da sace sacen jama’a da ake yi inda kuma ake tilasta masu biyan diyya wanda hakkan kan sa su sayarda kadarorinsu kama daga Shanu da abinda suka mallaka.
Kafin dai rundunar ‘yan Sandan jihar ta Ogun ta bayana ceto ita wannan tsohowar minister da aka yi garkuwa da ita tun da farko sai data yi shelar bada lada har Naira miliyan biyar ga duk wani labari da ya kai ga gano Ministar da akayi garkuwa da ita kawo yanzu dai babu tabbacin cewa an biya kudin fansa ga wadanda suka yi garkuwa da wannan tsohuwar Minista suka nema, na kusan Naira miliyan dari biyu.