Wani sabon bincike ya nuna gagarumin bambanci tsakanin ‘yan jam’iyyar democrat da republican da ke nan Amurka akan yadda shugaban kasan mai zuwa zai tattauna batutuwan masu tsattsauran ra’ayin addinin musulunci.
Cibiyar binciken Pew ta gano cewa kashi 65 na ‘yan republican, ko masu mara masu baya, na son wanda zai gaji shugaba Barack Obama ya yi magana gaba gadi akan tsattsauran ra’ayin addini, ko ma da bayanan sun caccaki addinin Islama. Amma kashi 70 din ‘yan democrat, ko magoya bayansu na ganin ya kamata wanda zai gaji shugabancin Amurka ya bi sannu a hankali akan batun tsattsauran ra’ayin addini.
Baki daya dai kusan rabin Amurkawa na son wanda zai gaji shugabancin kasar kada ya soki addinin Islama akan tsattsauran ra’ayin addini.
Binciken da aka gudanar cikin watan da ya gabata, ya kuma gano cewa kusan rabin wadanda aka tambaya na ganin cewa wasu musulmai ‘yan Amurka na da dabi’un kinjinin Amurka, ciki har da kashi 11 na wadanda suke ganin cewa yawancin musulman Amurka ba sa son Amurka.