Print
Sanata Bala Ibn Na'Allah ya sa 'yansanda suka kama wani malamin makaranta Abubakar Meli a garin Kebbi, Jihar Kebbi.
No media source currently available
Matsalar harbi da bindiga da aka samu a wata makarantar sakandare a Georgia, wata matashiya ce dake nuna yadda makamai suka fi yin sanadin mutuwar mutane a Amurka fiye da a sauran manyan kasashe da suka ci gaba, a cewar kwararru.
Gabanin zaben shugaban kasar na Amurka, manyan jam'iyyun siyasar kasar guda biyu suna nuna damuwa game da sahihancin zaben – wato abubuwa da suka shafi rijistar masu zabe, da kada kuri’a da kuma kirga kuri’u da tabbatar da kuri'un, da ma batun magance duk wasu muhimman batutuwan da za su iya tasowa
Amfani da kwayoyin rage Zafin ciwo ba bisa ka'ida ba ya ci gaba da kasancewa cikin abubuwan da ke kan gaba akan matsalar jaraba a fadin duniya. Bari mu leka Najeriya inda sama da mutum militan 14 suke ta'ammalı da kwayoyi ba bisa ka'ida ba, kamar yadda alkaluman hukumar NDLEA a kasar suka nuna.
Ruwan sama mai yawa da kuma fashewar da wata madatsar ruwa ta yi a jihar Borno sun haddasa mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, lamarin da ya sanya ruwa ya shanye gidaje da ma’aikatu da sauransu a birnin. Gwamnatin kasar ta sha alwashin taimakama wadanda ambaliyar ta shafa.
'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan karin farashin man fetur a kasar, wanda kawo yanzu ya sanya farashin sauran kaya kara tashi a kasuwanni. Karin farashin man fetur daga Naira 568 da 617 zuwa Naira 850 da 1,400, ya sa kudin mota ya rubanya a wasu wurare, yayin da kayan abinci su ma suka daga.
To shin ya ya masana siyasar duniya suke Kallon wannan muhawara tsakanin tsohon shugaban kasa Donald Trump da kuma Kamala Harris? Haruna Shehu Marabar Jos ya tattauna da Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, Malami A Jami’ar Abuja.