Wasu 'yan Najeriya, da wasu kwararru daga cikinsu, sun fara maida martani kan matakin dage zaben kasa a Najeriya wanda , aka shirya za'a fara ranar Asabar 14 ga watan nan.
Wani malami a Jami'ar kimiyya da Fasaha ta Modibbo Adama dake Yola, fadar jihar Adamawa, Dr. Keftin Amuga Namala, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, a cikin hira da suka yi cewa, a matsayinsa na wanda yayi siyasa a baya, abunda zai ce shine 'yan Najeriya su kai zuciya nesa, saboda a ganinsa ana neman yadda za'a takali jama'a ne.
Gameda dalilan tsaro da aka bayar a zaman hujjar dage zaben, keftin Amuga yace ai wannan abun kunya ne. Yace tun yaushe ake tatsuniyar za'a gama da 'yan Boko Haram, amma har yanzu suna nan.
Shi kuma a nasa ra'ayin, kakakin jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Rev. Fadiyo, yace su fa ba zasu tsorata ba,kuma ko yaushe aka gudanar da zaben nan, da ikon Allah sune zasu kafa gwamnati.
Daga nan ya baiwa 'yan Najeriya shawara cewa su kai zuciya nesa, kada su yarda su karya doka. Yace duniya duka tana kallo, kuma Allah Shima yana gani. Ba zai yarda a ci gaba da zaluntarsu ba.
Ga rahoton.