A lokacin da yake bayyana lamarin ne a gaban manema labarai a birnin Tarayya Abuja Asabar dinnan, shugaban Hukumar, Attahiru Jega yace za’a gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisu ran 28 ga watan Maris, sannan a gudanar dana gwamna da ‘yan majalisar jihohi ranar 11 ga watan Afrilu.
Mr. Jega yace an dage ranar zaben ne, saboda jami’an tsaro sun bayyana cewa baza su bada kariya ba ranakun 14 da 28 na watan Fabrairu.
Shugaban INEC yace jami’an tsaron sun gayawa hukumarshi cewa zasu fara yaki na musamman na makonni shida akan Boko Haram ne a arewa maso gabashin Najeriya, saboda haka ‘yan Najeriya basu bukatar harkokin zabe ya dauke musu hankali.
Mr. Jega ya bayyana cewa jami’an tsaron zasu fara ayyukansu ne ran 14 ga watan Fabrairu, ranar da INEC ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya.
Mr. Jega ya kara da cewa babu wanda ya tursasawa hukumarshi dage zaben, yake cewa tunda jami’an tsaro baza su iya samar da tsaro ba, bai kama INEC ta saka rayukan ma’aikata kusan 700,000 a cikin hadari ba.
Attahiru Jega ya kara da cewa sauya ranar zaben ba zai kara adadin kudaden da ta kasha ba wajen shirya zaben.
Sai dai jam’iyyun adawa sun nuna rashin amincewarsu da wannan dagewa, suna ganin hakan a matsayin wata makarkashiya na yin magudi.