A Indonesia yawan wadanda gocewar laka ta halaka bayanda ta lalata wani kauye, yanzu ya haura daga takwas zuwa 17, yayinda masu aikin ceto suke ci gaba da zakulo gawarwaki daga cikin turbayar da kuma baraguzai.
Kusan mutane dari ne har yanzu ba’a san inda suke ba, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwariya da ya fara a daren jiya jumma’a a a kauyen Jemblung a wata gunduma dake lardin Java dake tsakiyar kasar. Lakar ta kwashe fiyeda gidaje dari. An kwashe wasu daruruwan mutane daga yankin.
Hukumar agajin gaggawa ta kasar tace an ceto mutane 15, amma an kwantarda 11 daga cikinsu a asibiti. Hukumar tace daruruwan mutane, cikinsu har da ‘Yansanda da sojoji da kuma da mazauna yankin suna tono cikin turbayar da hannayensu wasu da shebura, da faratanu suna neman wadanda suka bace.
Karin ruwan sama a yau Asabar ya hana ci gaba da aikin ceto. An kawo manyan na’urorin aiki do,in taimakawa da ayyukan ceto.
Damuna ta sauka a Indonesia alokacin gocewar laka sakamakon ruwan sama ya zama ruwan dare.