Wannan dai itace barazanar baya-bayan nan daga cikin irinta masu yawa da Koriya ta Arewa ta sha yiwa Amurka da kawayenta a kwanan nan.
Sai dai ba’a jin cewa Koriya ta Arewa tana da fasahar da zata iya harbo duk wani makamain da zai iya kawowa kan Amurka.
Wannan zare idanun na baya-bayan nan ya biyo ne bayan jan kunnen da shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-hye tayi wa ta Arewa din da cewa ta watsarda shirinta na neman kera makaman nukiliya kuma ta daina yi wa mutane wani zazzare ido da barazana; har tace sai ta haka ne kawai Koriya ta Arewa zata tsirad da kanta.
Shugabar tayi wannan gargadin ne a wajen wani taron tuna kamallar shekaru ukku da nutsarda wani jirgin yakin Koriya ta Kudu mai suna Cheonan wanda kuma Koriya ta Kudu ke dora laifin nutsar da shi akan Koriya ta Arewa, har sojan ruwa 46 na Koriya ta Kudu suka hallaka.
Koriya ta Arewa ta musanta nutsar da jirgin.