Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma Ya Sauka Daga Mulki


Hoton Papa roma kennan.
Hoton Papa roma kennan.

Paparoma mai barin gado Benedict ya gana da manyan Fadojinsa na Vatican, sannan ya dare kan jirgin saman da ya kai shi wajen da zai soma hutawarsa a wajen birnin Rome, inda kuma daga nan ne zai soma ritayar shi ta barin aiki.

A cikin jawabin ban kwana da yayi, wanda kuma aka nuna ta tashar telebijin ta Vatican, Paparoman yayi alkawarin cewa zai zama mai “cikakkiyar biyayya” ga sabon paparoman da zai gaje shi.

Wannan kalamin nasa zai bada kwanciyar hankali ga masu sukar lamirin cewa mai yiyuwa ne kasancewar Paparoman da yayi ritaya a raye zai iya rage kimar sabon Paparoman da zai kama ragamar mulkin cocin ta Katolika ta duniya.

Ana sa ran wannan rana ta yau Alhamis ta kasance ran ace ta hutawa da natsuwa a wurin paparoma Benedict.

Ritayarsa dai zata fara ne daga karfe 8 na marecen yau, agogon Rome.

Daga wannan lokacin ne kofofin fadar Castel Gandolfo zasu rufe kuma daga nan ne dogarawan dake gadinta zasu janye.
XS
SM
MD
LG