Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makamin Nukiliya Na 3


Shugaba Kim Jong-Un na Koriya Ta Arewa yana jagorancin taron majalisar sojojin kasar
Shugaba Kim Jong-Un na Koriya Ta Arewa yana jagorancin taron majalisar sojojin kasar

Hukumomi a Pyongyang sun ce su n yi wannan gwajin ne a saboda "mummunar kiyayyar" da Amurka ta ke nuna ma kasar.

Koriya ta Arewa ta ce ta samu nasarar gudanar da gwaji na uku na makamin nukiliya, a bayan da ta sanya kafa ta yi kutufau da gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata na cewa ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar ya fada yau talata cewa an yi amfani da wani dan karamin kundun nukiliya, amma mai tsananin karfi, wajen gudanar da wannan gwaji na karkashin kasa. Yace an gudanar da wannan gwajin ne a saboda "mummunar kiyayyar" da Amurka take nuna musu.

Ma’aikatar tsaron Koriya ta Kudu, wadda ta kara zaman shirin ko ta kwana na sojojinta, ta tabbatar da cewa da gaske ne an tayar da wani bam na nukiliya yau talata a kusa da inda Koriya ta Arewa ta gudanar da gwaje-gwajenta na baya.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yayi gaggawar yin tur da wannan matakin da ya bayyana a zaman "na neman tayar da zaune-tsaye", yana mai bayyana shi a zaman keta takunkumin da kasashen duniya suka sanya ma kasar.

Shugaba Barack Obama na Amurka, ya bayyana gwajin a zaman matakin mummunar tsokana, yana mai fadin cewa yin barazana ce ga tsaron Amurka da kuma zaman lafiyar duniya. Yayi kiran da kasashen duniya su dauki matakan gaggawa masu ma'ana da nagarta na mayar da martani.

Wakilin Muryar Amurka a Tokyo, Steve Herman, yace ma’aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta sanya ido domin ganin ko Koriya ta Arewa zata yi karin fashe-fashe ko harba makamai masu linzami.

Jami’an diflomasiyya a Majalisar Dinkin Duniya sun ce za a yi zaman gaggawa na Kwamitin Sulhu yau talata da safiya a New York.
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG