A lokacin da yake jawabi ga mabiya darikar Roman katolika da suka cika majami’ar St. Peter dake fadarsa ta Vatican cikin daren litinin, Paparoman yayi kira da a kawo karshen zub da jini a kasashen Sham da Lebanon da Iraqi da makwabtansu. Har ila yau yayi addu'ar ganin yahudawa da Falasdinawa sun zauna da juna cikin lumana.
Dubban masu ziyara daga sassa dabam-dabam na duniya sun hallara a garin Bethlehem na yankin Yammacin kogin Jordan a wurin da kiristoci suka yi imanin an haifi Yesu.
Musamman bukukuwan kirsimeti na bana sun zo cikin lokacin murna da farin ciki ga masu masaukin baki, Falasdinawa, wadanda a watan da ya shige Majalisar dinkin duniya ta amince da yankinsu a zaman ‘yantacciyar kasar Falasdinu.
A cikin hudubarsa ta jajiberen kirsimeti, babban bishop na ‘yan darikar Roman Katolika a yankin Falasdinu, Fouad Twal, yayi murnar wannan nasarar da Falasdinawa suka samu, yana kuma kira a garesu da su yi aiki tare da ‘yan Isra’ila domin kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin.