Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhu Zai Jefa Kuri'a Kan Kwango-Kinshasa


'Yan tawayen M23 a lokacin da suak shiga Goma, talata 20 Nuwamba, 2012.
'Yan tawayen M23 a lokacin da suak shiga Goma, talata 20 Nuwamba, 2012.

'Yan tawayen M23 sun kama birnin Goma dake bakin iyakar Kwango da Rwanda talata, yayin da sojojin gwamnati suka gudu.

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yana shirin jefa kuri'a kan wani daftarin kudurin da kasar Faransa ta gabatar, wanda ke neman 'yan tawaye a kasar Kwango-Ta-Kinshasa su janye daga birnin Goma, tare da kafa takunkumi a kan shugabannin 'yan tawayen.

Talata dakarun 'yan tawaye na kungiyar M23 suka kwace wannan muhimmin birni dake bakin iyaka da Rwanda ba tare da turjiya ba. Sojojin gwamnatin Kwango sun gudu, yayin da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su dubu daya da dari biyar suka tsaya kawai su na kallo.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, yace abin kunya ne a ce akwai sojojin kiyaye zaman lafiya su dubu 17 a cikin kasar Kwango, amma sun kasa hana wasu 'yan daruruwan mutane kwace wannan birni. Yayi kiran da a sake nazarin tsarin aikin sojojin kiyaye zaman lafiyar.

Amurka ta yi kiran da a gudanar da tattaunawa a tsakanin Kwango da makwabtanta Rwanda da Uganda. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland, ta ce Washington tana aiki tare da shugabannin Kwango da Rwanda domin kafa wani tsarin siyasa na warware batun.

Kwango ta Kinshasa ta ce ba zata tattauna kai tsaye da kungiyar M23 ba sai idan an hada da kasar Rwanda a ciki. Shugaba Joseph Kabila na Kwango yana zargin Rwanda da laifin goyon bayan 'yan tawayen, zargin da wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ma ya gaskata shi. Shugaba Paul Kagame na Rwanda ya musanta wannan zargin.
XS
SM
MD
LG