Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nkosazana Dlamini-Zuma Ita Ce Sabuwar Shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka


Sabuwar hedkwatar Kungiyar Tarayyar Afirka a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.
Sabuwar hedkwatar Kungiyar Tarayyar Afirka a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Dlamini-Zuma ta doke wanda ke kan kujerar, Jean Ping, a bayan an shafe zagaye hudu ana zabe a wurin taron kolin Kungiyar a Addis Ababa

Shugabannin Afirka sun zabi ministar harkokin cikin gidan Afirka ta Kudu, Nkosazana Dlamini-Zuma, a zaman sabuwar shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka, ta zamo macen farko, kuma 'yar Afirka ta Kudu ta farko da ta taba rike wannan mukami.

Dlamini-Zuma ta doke shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka mai ci, Jean Ping, bayan zagaye hudu na jefa kuri'a jiya lahadi a wurin taron kolin kungiyar a Addis Ababa a kasar Ethiopia.

Ita ce tsohuwar matar shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma.

A can baya, wannan mukami na shugabancin Kungiyar Tarayyar Afirka ya kan fada hannun wani jami'in gwamnati daga wata karamar kasa a nahiyar ne. Dlamini-Zuma ta ce babu wata alaka a tsakanin fitowarta daga babbar kasa kamar Afirka ta Kudu da kuma wkadayinta na bayar da gudumawa ga Kungiyar.

Kungiyar Tarayyar Afirka tana takalar wasu fitinu a sassan nahiyar. Tana nazarin yiwuwar tura sojoji domin su yaki 'yan tawaye dauke da makamai a kasar Kwango-ta-Kinshasa. Har ila yau tana goyon bayan shirin kasashen Afirka ta Yamma na yakar masu kishin addini a yankin arewacin kasar Mali.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG