Rundunar sojan Nijar ta shaida wa wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka cewa, za su kashe Bazoum idan kasashen da ke makwabtaka da kasar suka yi yunkurin shiga tsakani na soji don maido da mulkinsa, kamar yadda wasu jami’an kasashen yammacin duniya suka shaida wa kamfanin dillancin labaran AP.
Tun bayan da sojoji masu gadin fadar shugaban kasa suka tsare shugaba Mohamed Bazoum a ranar Laraba 26 ga watan Yuli, sannan daga baya suka sanar da yin juyin mulki, abubuwa da dama sun faru.
Mun duba wata hira ta musamman da Muryar Amurka ta yi da Shugaba Mohamed Bazoum a 2021, inda shugaban ya bayyana ra'ayinsa akan abinda ke kawo juyin mulki a wasu makwabtan kasar.
Akan wannan dambarwa dake faruwa a Nijar, mun samu tattaunawa da jakadan Nijar din anan Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri.
A wani taron gaggawa da ta yi a Abuja a kan juyin mulkin a Nijar, kungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin kasar wa’adin mako guda da su mayar da gwamnatin Mohamed Bazoum ko kuma ta dauki dukkan matakin da ya dace – wanda ya hada da yiwuwar amfani da karfin soji.
Sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar sun sanar da kwamandan sojojin dake gadin fadar shugaban kasar ta Nijar Abdourahmane Tchiani a matsayin jagoran gwamnatin kasar.
Duba tarihin juyin mulki a kasar Nijar, wannan dai shi ne karo na biyar da sojoji ke yin juyin mulki tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960