Kungiyar dattawan Arewa ta yi tsokaci kan wani sabon yanayi mai cike da hadari inda wasu ’yan siyasa ke jawo hankalin masu kada kuri’a su sayi katin zabensu na din-din-din a shirye-shiryen zaben 2023 mai zuwa.
A cigaba da yakin neman zaben sabon shugaban Najeriya a ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da magoya bayan su na bayanan abubuwan da a ke ganin za su haddasa mu su cikas.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar Litinin 12 ga watan Disemba a matsayin ranar da za’a fara karbar katin zabe.
Madugun kamfen din samun tikitin dan takarar APC Bola Tinubu, Babachir David Lawan ya fito karara ya ce bai ga yadda Tinubu zai lashe zaben 2023 ba tun da bai dauki kirista mataimaki ba.
Jam’iyyar Lebour ta sanar da rasuwar mataimakin shugaban Jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya, Adi Shirsha .
Batun kiyaye laffuza da kalamai yayin tallar ‘yan takara na daga cikin muhimman abubuwan da suka mamaye jawaban shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawal ya amince da Bashir Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben Sanatan Yobe ta Arewa a shekarar 2023.
Duk da bude damar fara yakin neman zabe da hukumar zaben Najeriya ta INEC ta yi, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da ke alwashin shiryawa tsaf don tinkarar zaben 2023 ba su kaddamar da kamfe ba.
Jam'iyar APC mai mulki a Najeyatana ci gaba da fuskantar barazanar ficewar ‘ya'yanta zuwa wasu jam'iyu, daidai lokacin da jam'iyun ke faman samun jama'a don cin zabubukan shekara ta 2023.