Najeriya dai ta na fama da matsalar tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru da dama, abin da ya haifar da kunci, wahala da damuwa a tsakanin ‘yan kasar.
'Yan takarar shugabancin Amurkan Joe Biden da Donald Trump su na ci gaba yakin neman kuri’un bakar fata a zaben dake tafe. Babban editan Muryar Amurka, Scott Stearn, ya duba yadda ‘yan takarar ke zawarcin kuri’un Amurkawa ‘yan asalin Afrika.
To a cikin shekara guda, gwamnatin ta shugaba Tinubu a Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan fashin daji da sauran ‘yan ta’adda kimanin 9500, sannan ta kama wasu kimanin dubu bakwai a yakin da take yi da matsalar tsaro.
To yayin da al’umma Musulmi a fadin duniya ke ci gaba da shirye-shiryen babbar sallah, Wakiliyar muryar Amurka, Baraka Bashir ta ziyarci wasu kasuwanni dabbobi a Kano don jin yadda hada-hadar ragunan layya ke tafiya a lokacin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke shirye-shiryen babbar sallah.
Yayin da muhawarar sabon albashi mafi karancin ke wakana, wasu mazauna Abuja a Najeriyar sun bayyana ra’ayoyinsu game da adadin da suke gani yakamata a rika biyan ma’aikata saboda halin da tattalin arzikin kasar ya ke ciki a halin yanzu.
Wata kwararriya a Maiduguri, Dr Aida Abba Wajes ta yi karin haske akan illolin gurbatacciyar iska ga lafiyar mutane da kuma matakan da za a iya dauka.
Domin Kari