A arewa maso gabashin Najeriya, manoma a Zabarmari dake jihar Borno, wadanda suka rasa ‘yan uwansu su kusan hamsin da mayakan Boko Haram suka hallaka a watannin baya, sun samu kwarin gwiwar komawa gonakinsu, bayan da gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanya mafarauta su ba su kariya.