Matsalar tsaro da annobar COVID-19, na daga cikin manyan kalubalen da suke haifar tarnaki ga kasashen nahiyar Afirka da dama, kamar yadda shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Congo Felix Tshisekedi ya ce.
Wannan lamari ya sa wakilin Amurka na musamman a Haiti ya ajiye aikinsa yayin da ake sukar matakan da gwamnatin Biden ta dauka akan bakin hauren.
Bikin Lasar Gishiri, dadaddiyar ala’ada ce da Fulanin yankin Agadez suka jima suna yi a kowacce shekara.
Labarin zababben kansila da ya rungumi sana’ar sayar da shayi a Kano, wanda ya ke karfafa gwiwar sauran matasa da kar su rika raina sana’ar yi.
Wannan biki ya tattaro 'yan kabilar ta Tubawa har daga wasu kasashen waje inda aka yi kade-kade da baje kolin kayayyakin al'adu na gargajiya.
Matsalar masu yin ba-haya a waje a Najeriya, matsala ce da ta jima tana ci wa hukumomi tuwo a kwarya.
A sassan duniya musamman a kasashe masu tasowa wasu kan nuna tsangwama ga mutane masu nakasa ta hanyar nuna cewa ba za su iya gudanar da wasu ayyuka kamar mutane masu lafiya ba.
Miliyoyin mutane rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da wasu yankunan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya a cewar hukukomi.
Samun sabon kwamishinan na 'yan sanda na zuwa ne yayin da ake samun daruruwan mayakan kungiyar ta Boko Haram da ISWAP suna mika wuya.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce daukan mataki a jiha guda ba kai kai kasar ga gaci ba a kokarin da ake yi na magance matsalar tsaro.
Hukumomin Amurka sun dauki matakan gaggawa ne a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar wacce rahotanni suka nuna tana bazuwa a hankali.
Wasan tseren takalmin taya na kara karbuwa a wasu kasashen Afirka duk kuwa da cewa matasa da ke nuna sha'awar wasan kan fuskanci kalubalen samun kayan yin atisaye.
Domin Kari