Tashin farashi ko tsadar naman miya, na neman maida fatar sa wacce aka fi sani da Ganda ko kpomo a wasu harsuna, maye gurbin nama a wasu gidaje, da kuma wuraren sayar da abinci. Fatima Saleh Ladan na dauke da karin bayani a wannan rahoto.
Yayin da yake shirin kammala wa’adin mulkinsa, Shugaba Joe Biden ya kulla wata sabuwar dangantaka tsakanin Amurka da nahiyar Afirka. A cikin wannan fassarar rahoton wakiliyar Muryar Amurka a Fadar White House Anita Powell, Biden ya kafa tarihi a ziyarar da ya kai kasar Angola.
Masu saka hannun jari a kasuwar Crypto na da kwarin gwiwar bunkasar fannin karkashin shugabancin Donald Trump wanda a yakin neman zabensa a wannan shekarar ya nuna goyon baya ga wannan nau'in kudade na yanar gizo. Ga fassarar rahoton Scott Stearns.
Har yanzu muna kan batun zaben na Ghana inda Hukumar zabe kasar ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryenta da suka hada da raba kuri’un zabe a fadin kasar. Hamza Adam ya tattauna da Sheriff Issah Abdul Salam, wani mai sharhi kan siyasa game da gaskiyar wannan ikirari da hukumar ta yi.
Shekaru 10 da suka gabata, kashi 80% cikin 100 na 'yan Afirka sun yi imanin cewa dimokuradiyya ita ce mafi kyawun tsarin mulki, sannan a kowanne yanayi sun gwammace su yi zabe akan mulkin soji ko na mutum daya. Amma wannan adadin ya ragu zuwa 66% cikin 100 a yanzu.
Domin Kari