Tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce yana jagorantar wani shiri na tattara bayanan asarar rayuka da dukiya da al'ummar arewa suka yi don neman diyyar da ta kai Naira tiriliyan bakwai.
TAMBAYA: Menene ku ke so a tabo a wannan zaman musayar miyau?
Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta kasa da kasa Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya su daina rufa-rufa kan batun kisan gillan da aka yi wa masu zanga a gadar Lekki.
#EndSars: Duk da dokar hana fita da gwamnati ta sanya, mutane sun balle rumbunan abinci na gwamnati a Jos, inda suka yi ta kwasan kayan abinci.
Wasu matasa a Najeriya sun shaidawa Muryar Amurka dalilin da ya sa suka shafe kwanaki suna zanga zanga a birnin Jos.
Matasa sun kona motoci sannan suka lalata shaguna da wani banki a birnin Jos yayin zanga-zangar adawa da cin zarafin mutane da ake zargin ‘yan sanda a Najeriya na aikatawa.
Mutane suna zanga zanga a kan titunan biranen Jos, Abuja, da Legas na kin amincewa da cin zarafi da kuma kuntatawa al'umma da 'yan sanda ke yi.