An gudanar da taron karfafawa al’ummar zanguna kwarin gwiwar kasuwanci ko Zongo Startup Summit 2023, tare da yin kira ga matasa da su kasance masu halayen da suka dace, domin samun nasarar kasuwancinsu.
Wannan kudiri da Majalidsar ta Wakilai ta sa a gaba ya sa masana tattalin arziki bayyana ra'ayoyin mabanbanta
Babban bankin ya ce yana gudanar da bincike bayan samun rahotannin da ke zargin bankunan kasar da hada kai da masu PoS wajen haifar da matsalar karancin naira, lamarin da ya ce yana shafar tattalin arzikin kasar.
Hukumar Kididdiga Ta Kasa a Najeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki a kasar ya kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da kasar ta ga hakan tun a shekarar 1996.
“Yanzu kan na yi nadama, in Allah ya yarda kuma ba zan sake yi wa wata mace a duniya kwalliya ba.” In ji Mansur Make Up.
Kasafin ya amince da sanya canjin dala a kan Naira 700 sai kuma gangar man fetur a kan dala 73.96.
Jihohin yankin na arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihar Borno, sun kwashe sama da shekara goma suna fama da matsalar mayakan Boko Haram.
Ministan ciniki da masana'antu, Kobena Tahir Hammond, ya sanar da wani muhimmin mataki da gwamnatin Ghana ta dauka na samar da dokar hana shigowa da kayayyaki sama da 20, ciki har da shinkafa da wasu kayayyakin da ake amfani da su a Ghana.
Kungiyar ta NUPENG ta yi watsi da zarge-zargen kungiyar direbobin tankar man.
Wannan mataki da Najeriyar ta dauka zai duba hanyoyin janyo hankulan masu saka hannayen jari kasar.
Najeriya wacce ita ce kasar da ta fi yawan arzikin mai a nahiyar Afirka na shigo da manta daga kasashen ketare saboda matatun manta uku ba sa aiki.
A makon da ya gabata Amurka ta fitar da gargadi ga ‘yan kasarta da ke zaune a Najeriya inda ta yi kira a gare su da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar "fuskantar barazana” a wasu manyan otel-otel din biranen kasar.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.