Kasuwannin hannayen jari a Amurka sun yi kasa a ranar Juma'a yayin da ake nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyaki da haraji, yayin da wani rahoto da aka sa ido sosai akai ya ba da mabanbancin ma’ana game da kasuwar aikin yi a Amurka.
Shugaba Trump ya yi nuni da cewa za'a sanya wasu karin haraji a makonnin masu zuwa.
Kamfanin Tiktok na fuskantar wata dokar Amurka da ta umarce shi ya raba gari da mamallakinsa na kasar China Bytedance ko kuma a haramta shi a Amurka.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya ba da sanarwar zai dauke wutar lantarki a wasu sassa na babban birnin tarayya Abuja, daga ranar 6 ga watan Janairu zuwa 20 ga wata na wannan shekara.
Matsayar da aka gabatar a ranar Talata, za ta sasanta karar da ta shafi zargin cewa kamfanin na Apple ya saita na’urar ta Siri da gangan domin ta rika nadar tattaunawar mutane ta hanyar wayoyin salula na iPhone, da sauran na'urorin da aka sanya musu ita tsawon fiye da shekaru goma.
A karkashin jagorancin dan kasuwar mai kwarjini na tsawon shekaru 40 har zuwa 2021, yawan cinikin kamfanin ya rubanya har sau 10.
A bara Birtaniya ta bayyana cewa za ta shiga cikin wannan babbar yarjejeniyar ciniki tun bayan ficewar ta daga Tarayyar Turai.
Okonjo-Iweala ita ce mace kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara rike wannan mukami tunda aka kafa kungiyar.
A cewar NNPCL, hadin gwiwar wani muhimmin mataki ne na tabbatar da nasarar dorewar ayyukan matatar ta Dangote tare da inganta amfani da iskar gas a cikin Najeriya.
Yanzu dai kimanin makonni biyu kenan babu hasken wutar lantarki a daukacin yankin na arewacin Najeriya birni da karkara.
Domin Kari
No media source currently available