Tsarin inshorar da a ke kira Takaful ya kara samun tagomashin raba rarar kudi ga wadanda suka shiga tsarin da samun miliyoyin Naira.
Biyo bayan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi jim kadan bayan rantsuwar kama aiki na mayar da birnin kan taswirarta na asali, wasu masu kananan sana’o’i na neman a yi nazari kar a jefa su cikin matsin rayuwa.
Tashin farashin dala a Najeriya ya sa kayayyaki musamman na masarufi sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa al'umar kasar cikin halin ni-'yasu.
Daga cikin bukatun da kungiyar ta NLC ta gabatar, akwai neman a kara mafi karancin albashin ma’aikata.
Yayin da damina ke kankama a sassan Najeriya, Kungiyar Manoman shinkafa, sarrafa ta da kuma kasuwancinta ta Najeriya ta kaddamar da Shirin ta na bada lamunin kayan noma na musamman domin karfafa gwiwar manoma.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ci tarar Meta, babban kamfanin da ya mallaki Facebook, dala biliyan 1.3 tare da umartarsa da ya daina mika bayanan masu amfani da shafin zuwa Amurka nan da watan Oktoba.
Sai dai kungiyar Malaman jami'a ta ASUU ba ta ji dadi ba, ganin yadda aka cire su cikin wadanda za su ci moriyar wannan kari.
Cibiyar kula da harkokin tattalin arziki ta bayyana damuwarta game da maimaita kura-kurai da gwamnatoci suka yi a baya wanda ya sanya tattalin arzikin Ghana ya tabarbare tsawon shekaru.
Domin Kari
No media source currently available