Shirin kasuwa na wannan makon ya kai ziyara wasu kasuwannin jihohin jamhuriyar Nijer gabanin bukukuwan Sallah.
Farfesa Nail Muhammad Kamil babban lakciran ilimin kasuwanci a Jami'ar kimiyya da fasaha ta "KNUST" ya ce mamayar da Rasha ke yi a Ukraine na tasiri sosai akan farashin kayayyaki a duniya.
Ya yi jawabin ne a wajen taron kasuwanci na Afirka karo na 24 da makarantar kasuwanci ta Harvard ta shirya.
Shirin Kasuwa na wannan makon ya kai ziyara babbar kasuwar Timber Market da ke birnin Accra a kasar Ghana.
Wani Ma’aikacin kamfanin Dangote ya ce a wannan watan matatar man za ta fara aiki a kwata na hudu na shekarar 2022.
Masu sana’ar a bakin titin birnin Accra a Ghana sun roki Ministan da ya nema musu sabon wuri kafin ya kori su daga hanyar titin.
Fadar shugaban Najeriya ta bayyana kamfanin takin na Dangote a matsayin mafi girma a duniya.
Shugaban kula da dokokin ma'aikatar man fetur ta Najeriya, Malam Faruk Ahmed, ya yi cikakken bayani a game da akasi da aka samu a game da gurbataccen man fetur a wasu sassan kasar.
Hukumomin jihar sun ce kowane Keke Napep na dauke da wani tambarin na’ura da zai rika bibiyar duk inda aka je da abin hawan da zimmar tabbatar da ana amfani da shi bisa ka’ida.
Dogayen layuka a gidajen mai na daga cikin alamun da ‘yan Najeriya ke la’akkari da su wajen yiwuwar samun karancin man fetur a kasar.
A farkon makon nan gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa ta janye shirin cire kudaden tallafin mai.
Matasa da matasan sun koyi sana’o’i irinsu hada man shafawa da na amfanin gida da sauransu.
Domin Kari
No media source currently available