Jihar Penssylvania na da matukar muhinmanci a siyasar Amurka.
Zababben Shugaban Amurka, Joe Biden, na shirin gabatar da albishir ga al’ummar kasar, da kuma inda kasar zata dosa a ranar Laraba, lokacin rantsar da shi.
Ana ci gaba da shirye shiyen mika mulki ga sabuwar gwamnati a Amurka, al’amarin da ya biyo bayan wasu batutuwa da dama, ciki har da abkawa ginin Majalisar dokokin kasar, inda har aka yi jina-jina da mace mace.
An samu bullar sabon nau'in cutar COVID-19 na Birtaniya a Garin Los Angeles da ke jihar California a Amurka.
Yayin da tashin hankalin kungiyoyin bata gari, rashin ayyuka, da talauci suka addabe su, ayarin bakin na fatan isa Amurka don samun rayuwa mafi kyau.
Hukumomin tsaro kulle birnin Washington kana jami’an tsaron Amurka suna kara jan damarar tinkarar magoya bayan Trump da za su yi tattaki a manyan biranen jihohin Amurka 50 a karshen wannan mako.
A cikin sa’o’in farko da ya zama shugaban kasa, Joe Biden zai yi amfani da ikon shugaban kasa ya sauya wasu matakai masu tsarkakiya da Trump ya dauka a baya kana ya fara daukar matakan magance annobar coronavirus, inji shugaban ma’aikatan ofishin shugaban kasa mai jiran gado a jiya Asabar.
An rufe wasu tituna a kewayen ginin majalisar dokokin Amurka an kuma rufe wasu wuraren tarihi a birnin yayin da ake shirin rantsar da shugaba Joe Biden mai jiran gado ranar 20 ga watan Janairu.
A ci gaba da dauke hankalin duniya da abkawa Majalisar Dokokin Kasar Amurka da kuma tsige Shugaba Donald Trump karo na biyu da ya biyo baya, masana harkokin siyasar duniya na ci gaba da tsokaci game da tasirin wannan al'amarin.
Hukumomi a Amurka sun tsaurara matakan tsaro a birnin Washington DC yayin da ya rage kwanaki a rantsar da zababben Shugaba Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46.
A karo na biyu cikin wa'adin mulkinsa na shekaru hudu Majalisar Wakilan Amurka ta sake tsige shugaban kasa Donald Trump. Kuma zai fuskanci shari'a a Majalisar Dattawa bayan sabon shugaban kasa ya fara aiki.
Sabanin yadda a baya aka yi ta muhawara, kan ko shugaban kasa zai iya yafe wa kansa laifi, yanzu abin ya zama muhimmiyar muhawara tun bayan da magoya bayan Trump su ka fusata tare da afkawa ginin Majalisar Dokokin Amurka.
Domin Kari