Karfi da Hakkokin Gwamnatoci a Kowane Mataki.
A mafi yawan jihohi an samu inganci kan yadda aka gudanar da zabuka musamman ma ta fannin isar kayayyaki akan kari da kuma na'urar tantance masu zabe, sai dai an samu karancin masu zuwa kada kuri'u.
A yanzu haka ana jiran sakamakon zaben gwamna da 'yan majalisun jiha a ga matasa da mata nawa ne za su kai labari.
Yayin da aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya, rahotanni na cewa an samu karancin masu kada kuri'u a jihohi da dama ciki har da jihar Niger.
To da yake matasa sun samu baki sosai a babban zabe dake gudana a Najeriya, Ahmed Adamu shine shugaban kungiyar matasan kasashen da Britaniya ta raina.
Wata sabuwar dambarwa tsakanin jam'iyar APC da PDP ta taso a wasu jahohin Najeriya daf da lokacin zaben gwamnoni ke karatowa har ma a ganin wasu 'yan jam'iyar, ta can can ci tukwici.
Yayin da shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara jahar Adamawa da jahar Gombe domin karbar wasu 'yan jam'iyar PDP masu canza sheka wadanda suka hada da wasu tsofaffin gwamnoni, Yan jam'iyar APC sun nemi a basu kujerar majalisa.
Batun canja sheka a Najeriya ya fara zama ruwan dare yayin da ake tunkarar zauban gwamnoni da za gudanar a karshen mako mai zuwa.
Yayin da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi ke karatowa jam'iyyar, APC tana zargin PDP da kammala shirin tafka magudi a jihar Neja.
A bayan da 'yan Najeriya da shugabannin duniya cikinsu har da shugaba Barack Obama na Amurka, suka yaba da yadda ya tsara zaben 2015, shugaban hukumar zaben Najeriya, Attahiru Jega, ya tattauna da Muryar Amurka kan dalilansu na amfani da sabbin dabarun hana yin magudi.
Domin Kari