Tsohon gwamnan jihar Filato, Ambasada Fidelis Tapgun, ya kwatanta masu ficewa daga PDP suna komawa jam’iyyar APC a matsayin ‘yan ci rani, ya na mai cewa hakan ba dai dai ba ne.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta shirya tsaf domin ganin cewa an gudanar da zaben gwamnoni da za’a sake gudanarwa a jahohin biyu na Abiya da Imo, a sakamakon matsalolin da aka fuskanta a zaben da ya gabata.
Rahotanni daga jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya, na cewa hukumar zaben jihar ta INEC ta ce ta shiryawa zaben raba gardama na gwamna da za a sake a jihar a ranar asabar mai zuwa.
A Najeriya, kotunan sauraren korafe-korafen zabe za su fara aiki, inda yanzu haka a Kano, jam'iyyar MPPP ke so soke zabukan da aka yi na 'yan majalisun tarayyan jihar.
Ganin irin kalubalen da ‘yan jarida suke fuskanta a ayyukansu a lokutan zabe, shiyasa Sashen Hausa na Muryar Amurka ya kawo shugabansa Leo Keyen domin yin fashin baki akan rawar ‘yan jaridu.
Yayin da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke shirye-shiryen mika mulki ga shugaba mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan gobe na Mayu, Jam’iyyar PDP ta shugaba mai barin gado tace ta daura damarar yin hamayya mai karfi ga sabuwar gwamnatin APC a kasar.
Yayin da rage makwanni kadan jam'iya mai mulki ta PDP ta mika ragamar mulkin kasar ga zababbiyar gwamnatin APC, Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ya yanke shawarar mika mulki a ranar 28 ga watan Mayu maimakon ranar 29.
Jam'iyun siyasa na APC da PDP sun amince da soke zaben wasu kananan hukumomi a jihar Imo amma sun ce hakan ba za ta sabu ba kan sakamakon jihar Rivers.
Mutanen Filato na Murnar Nasarar Dan Takarar Gwamnan APC
Jam'iyar APC tayi kira ga hukumar zaben Najeriya INEC da ta gaggauta soke zaben jahar Rivers da na Akwa Ibom a zargin sun tafka magudi.
Domin Kari