Yau anyi gangami na adua a kofar ofishin jakadancin Najeriya dage birnin Washington DC.
Bayan da suka kalli bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar wasu iyayen Chibok sun gane fuskokin 'ya'yansu a cikin bidiyon.
Domin tabbatar da cewa yara mata dake cikin bidiyon da Boko Haram ta bayyana daliban Chibok ne gwamnan Borno ya gayyato wasu daga cikin malaman makarantar da daliban da suka kubuta domin su gano fuskokin yaran dake cikin bidiyon.
Mahaifin daya daga cikin yaran da aka sace yace,yana farin ciki ganin hoton bidiyon da ‘yan boko haram suka fito dashi,domin ya ga wata mai kamar ‘yar sa a ciki.
Bai dace ba a koina a duniya ace an sarrafa rayukan yaran mutane wadanda bazu jiba basu gani ba akan rikicin da akeyi.
Daya daga cikin iyayen daliban Chibok ta tabbatar cewa ta ga 'yarta a cikin jerin yaran dake cikin hotunan bidiyon da mutumin dake cewa shine shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar a baya-bayannan.
Bayan wata daya da sace daliban makarantar 'yan mata dake Chibok a kudancin jihar Borno har yanzu shugaban kasar ya kasa ziyarar garin
A wani sabon bidiyo da mutumin da yace shine shugaban kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, ya fitar a baya-bayannan, Abubakar Shekau yace ya musuluntar da wadannan mata, wadanda yace ya sato su, sannan yana bukatar ayi musaya dasu.
Domin Kari