Masana tattalin arziki da siyasa suka ce ma'aunin tattalin arzikin da Najeriya ta canja ma kanta don a ce ita ce ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, na bagu ne kawai
Rikicin da ya faru a garin Ibi wanda ya kaiga rasa rayuka yasa gwamnatin jihar ta kafa dokar ba fita dare da rana.
Yayin da saura 'yan kwanaki wa'adin dokar ta baci da aka kakabawa jihohin Adamawa, Borno, da Yobe ke karatowa, gwamnoni johohin uku sun nemi gwamnatin tarayya ta cire dokar maikon sabuntata kamar yadda tayi a baya.
Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba, sun kai hari a garin Gwaram inda suka farma wani banki da ofishin 'yan sanda, kana suka jefa bam a kan wata kotu.
A wani taron manema labarai da kungiyar Miyetti Allah ta kasa ta kira a Abuja ta yi allawaai da harin da aka kaiwa rugagen Fulani a garin Keana cikin jihar Nasarawa.
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah da Kungiyar 'Yan Kudancin Kaduna ko SOKAPU sun sa hannu kan wata yarjejeniya domin kawo zaman lafiya a tsakanin al'ummominsu
Yanzu haka al-ummar yankin na cikin wani hali, sakamakon dokar hana fita waje na ba dare ba rana, da aka kafa yau kusan kwanaki hudu.
A halin da ake ciki batun sace wasu Italiyawa biyu da wata ‘yar Kanada daya, a kasar Kamaru, yanzu an baza sojoji, da jiragen masu saukar ungulu, da sojoji a kasa, da kuma babura suna zagaye ko zasu gano su.
Yayin da yake karbar daliban jihar Borno da suka dawo daga gasar karatun Kur'ani Mai Tsarki, gwamnan jihar yace karamin sani ya fi ciwo zafi kuma shi ne ya haifi kungiyar Boko Haram.
Idan ba'a anta ba bara ne jami'an tsaro a Najeriya suka farma wani gida a anguwar Apo dake cikin Abuja suka kashe wasu matasa takwas suka kuma raunata wasu da sunan cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne.
Mutum na biyu da ya kira kanshi sojan Najeriya, ya fito yayi korafi akan halin da rundunar sojan da yake tare da su ke ciki, dangane da yaki da kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram. Ibrahim Ka'almasih Garba na sashen Hausa ya tattauna da shi.
Domin kawo karshen rigingimun dake faruwa a jihar Taraba, shugabannin kabilun da abun ya sahafa sun lalubo bakin zaren warware matsalarsu.
Domin Kari