'Yan sanda a Rivers sun tsare mutanen ne da suka fito daga Jihar Jigawa bisa zargin cewa watakila su na da alaka da kungiyar Boko Haram
Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen sun gudu ne cikin kwanaki 10 da suka shige a sanadin hare-haren Boko Haram
Mutanen kauyukan Njaba da Kaya a Jihar Borno sun ce haka kwatsam suka ji karar harbe-harbe, sai kowa ya ranta cikin na kare.
Kwararru sun ce gazawa a yaki da Boko Haram it ace ta sa shugaba Goodluck Jonathan ya saukar da dukkan manyan hafsoshin kasar a makon da ya shige.
Sabili da yawan harin da ake kaiwa kan kayukan dake kewayen Maiduguri babban birnin jihar Borno mazauna kauyukan suna kauracewa suna shiga Maiduguri inda suke gudun hijira.
Farfasa Ango Abdullahi da yake magana da yawun dattawan arewa ya ce sun shaidawa shugaban kasa Goodluck Jonathan abubuwan dake faruwa kan tabarbarewar tsaro da cin zaluncin jama'ar arewa da makamantansu.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Borno, Lawan Tanko, yace mutanen biyu da aka kai ma farmaki malaman sakandare ne.
Bayan da hafsan sojojin Najeriya ya sauka daga mukaminsa kungiyar dattawan arewa ko AEF (Arewa Elders' Forum) a takaice, ta yi barazanar gurfanar da shi a gaban kotun kasa da kasa bisa ga zargin cin zarafin al'ummar arewa maso bagashin Najeriya da sunan yakar kungiyar Boko Haram.
Yayin da ake murnar samun zaman lafiya a jihar Taraba sai gashi wani rikici ya barke a yankin Donga da ya halaka rayuka.
'Yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kuma kona gidaje, suka kwace motoci a wannan gari mai tazarar kilomita 7 daga Maiduguri.
Kwamandan Rundunar ne ya bayyana haka a bikin maida kudin ga hanun 'yan kasuwan da aka yiwa fashi.
Kauyukan dake bakin iyaka da Najeriya a kasar Kamaru sun zamo kango a saboda kazamin fadan da aka gwabza a tsakanin sojojin Najeriya da 'yan Boko Haram a garin Banki na Jihar Borno