An kai wani mummunan harin kunar bakin wake a wani dakin karatu da ke cike da dalibai a Kabul babban birnin kasar Afghanistan da sanyin safiyar ranar Jumma’a, wanda ya yi sanadiyyar kisan akalla dalibai 19 kana ya raunata wasu 27. Cikin wadanda lamarin ya shafa har da 'yan mata.
Bayanai sun yi nuni da cewa guguwar za ta isa yankunan a ranar Juma'a zuwa wayewar garin Asabar.
Mazauna jihar Florida sama da miliyan biyu ne hukumomi suka ba umarnin su bar gidajensu yayin da guguwar Ian ke kusantar yankin.
Hukumomin Amurka sun kwashe shekaru suna son a dawo da shi Amurka domin fuskantar shari’a kan laifukan leken asiri.
Babban malamin addinin Musulinci, Sheikh Youssef al-Qaradawi, jagoran kungiyar 'yan uwa Musulmi kuma mai kare boren kasashen Larabawa, ya rasu a jiya Litinin yana da shekaru 96, kamar yadda aka wallafa a shafinsa na Twitter.
Sai dai bisa al’ada, mika mulki a Italiya kan dauki tsawon makonni kafin a rantsar da sabuwar gwamnati.
Hukumar NDLEA mai yaki da safaran miyagun kwayoyi ta Najeriua ta kama wasu masu safaran muggan kwayoyi da hodar iblis ko cocaine da yawansa ya kai na tan 1.8, ko kwatankwacin kilogram 1855 a birnin Lagos.
Hukumomin kasar Kamaru sun zargi ‘yan aware da yin garkuwa da wasu limaman cocin Katolika guda biyar, da wasu masu ibada daga wata coci da ke kan iyakarta da Najeriya a yammacin kasar.
Birtaniya da duniya sun yi bankwana na karshe ga Sarauniya Elizabeth ta biyu a jana'izar da ta sami halartar Shugabanni da Sarakuna da Firaministoci da kuma jama'a da suka yi dafifi a kan titunan birnin Landan don karrama Sarauniyar da ta shafe shekaru 70 tana mulki.
Guguwar Fiona ta afkawa gabar tekun Puerto Rico da ke kudu maso yamma a ranar Lahadi yayin da ta haifar da zabtarewar kasa, ta kuma kifar da na'urar wutar lantarki sannan ta tsaga kwalta.
Rahotannin sun ce akalla mutane 10 suka mutu yayin da wasu hudu suka bace bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a tsakiyar kasar Italiya, lamarin da ya sa batun sauyin yanayi ya zama da muhimmanci mako guda kafin zaben kasar.
Yayin da fadar masarautar Birtaniyya ta fitar da tsarin abubuwa da za a yi har zuwa lokacin jana'izar Sarauniya Elizabeth ta biyu, dubban mutane sun ja layi tun daga daren Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis don ganin akwatin gawar Sarauniyar a babban zauren taron Westminster.
Domin Kari