A wanan karon kamfanin ya shigar da karar ne a gaban cibiyar warware sabani da zuba jari da ake kira CIRDI inda yake neman a biyashi diyya dai dai da asarar da ya tafka a mahakar Uranium da ke arewacin Nijar
A zamanin wa’adinsa na farko, Trump ya yi amfani da manufar yin matsin lamba mai tsanani a kan Iran, inda ya janye Amurka daga shahararriyar yarjejeniyar nukiliyar nan ta 2015 wacce ta kakaba takunkumi a kan shirin nukiliyar Iran domin sassauta mata takunkuman.
Kamar yadda aka zaci zai faru, bayan da Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugaban kasa ya tsaurara sharuddan zama dan kasa, 'yan jam'iyyar Democrats sun ce ba za ta sabu ba.
Biyu daga cikin wadanda suka mutu sun rasa rayukansu ne a lokacin da suka duro daga benen don tsira da ransu.
A Lahadin da ta gabata aka saki mata ‘yan Isra’ila 3 domin yin musayar Falasdinawa fursunoni 90, sakamakon fara amfani da ‘yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Hamas.
Falasdinwa sun kewaye motocin na safa wasu kuma suka hau saman motocin sufa furta kalaman farin ciki.
Daga karshe dai Hamas ta bayar da sunayen, kuma Isira’ila ta ce za a fara tsagaita wuta da karfe 11:15 na safe.
An kama Seyni Amadou, babban editan gidan talabijin na Canal 4, in ji kungiyar CAP-Medias-Niger, mai wakiltar ma'aikatan yada labarai a kasar. A ranar Juma'ar da ta gabata ma'aikatar sadarwa ta Nijar ta sanar da dakatar da tashar ta shi na tsawon wata guda.
Majalisar zartarwar Isra’ila ta tabbatar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da sanyin safiyar yau Asabar a Gaza da kuma sakin mutanen da ake garkuwa da su domin kawo karshen yaki da Hamas na watanni 15.
Domin Kari