Al'ummar Australiya da New Zealand sun shiga sabuwar shekara ta 2025, har ma mazauna birnin Sydney da Auckland suka fara biki kamar yadda suka saba.
Najeriya da kasar Sin sun sake sabunta yarjejeniyar musayar kudade tsakanin su da ta kai yawan biliyan 15, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2, a wani yunkuri na karfafa cinikayya da zuba jari a tsakanin kasashen biyu
A yau Litinin Shugaban Koriya ta Kudu na riko, Choi Sang-Mok ya bada umarnin gaggauta duba lafiyar ilahirin ayyukan jiragen saman kasar a dai-dai lokacin da masu bincike ke aikin tantance mutanen da hatsarin jirgin sama mafi muni a kasar ya rutsa dasu, dama abinda ya sabbaba shi
Bincike ya nuna cewa asali Lakurawa mayaka ne da ke fada da zaluncin da suke ganin ana yi wa Buzaye da Fulani, wadanda suka yi suna kan dukiyar dabbobi da ke yawon kiwo a cikin dazuka, kafin daga baya su rikede su koma 'yan ta'adda.
To sai dai suna, da shaharar Carter, sun fito fili ne a rayuwar bayan shugabancinsa, wadda ita ce mafi tsawo da wani shugaban kasa ta rayu a tarihin Amurka.
Jimmy Carter ne shugaban kasar Amurka na farko da ya kai shekara 100 a duniya.
Akalla mutum 177 — mata 84, maza 82, da wasu 11 da ba a iya tantance jinsinsu nan take ba — suka mutu a hatsarin, a cewar hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu.
Akalla ‘yan Syria miliyan 3 ne suke neman mafaka a Turkiyya bayan da suka tsere daga kasar ta Syrai bayan da yaki ya barke a 2011.
An zargi dakarun tsaron kasar wadda ke yankin gabashin Afirka da kamawa da tsare mutane da dama ba bisa ka'ida ba, tun bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da matasa suka yi a watannin Yuni da Yuli.
Darakta-Janar na hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce bama-baman da suka fada kan ginin suna da matukar ta da hankali, ta yadda kunnuwansa suka yi ta rugugi har ‘yan kwanaki bayan harin.
Da ya ke tabbatar da ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zabe, Steinmeier ya jaddada bukatar samun “kwanciyar hankalin siyasa” sannan ya bukaci a gudanar da yakin neman cikin mutunci da kyautatawa”.
Domin Kari